Isa ga babban shafi
Togo

Mutane biyu sun mutu a tarzomar kasar Togo

Hankula sun kwanta a garin Mongo da ke arewacin kasar Togo, inda a jiya juma’a aka gudanar da tarzoma wadda ta yi sanadiyyar samun asarar rayukan akalla mutane biyu.

Shugaban Togo, Faure Gnassingbé
Shugaban Togo, Faure Gnassingbé AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Tarzomar dai ta barke ne bayan da hukumomin kasar suka bayar da izinin ware wani katafaren fili domin makiyaya a gabar ruwan wani kogi da ke yankin.

Manona da masunta da ke kiran kansu ‘yan asalin yankin sun nuna rashin amincersu da haka, inda daga bisani aka yi amfani da jami’an tsaro domin kwantar da hankula.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.