Isa ga babban shafi
MDD

Kasashe masu tasowa sun yi zarra wajen zuba jari

Majalisar Dinkin Duniya tace kasashe masu tasowa sun yi zarra wajen zuba jari fiye da sauran kasashen duniya musanman a fannin samar da wutar lantarki ta tsabtacacciyar hanya wanda kudin sa ya kai Dala biliyan 286 a shekarar 2015

Wuta mai anfani da hasken rana a kauyen Afrika
Wuta mai anfani da hasken rana a kauyen Afrika LA Bagnetto
Talla

Rahotan binciken na Majalisar Dinkin Duniya yace kasashe masu tasowa sun yi anfani da kusan Dala triliyan biyu da rabi wajen samar da wutar lantarki ta hanyar hasken rana, iska, rake da kuma wasu hanyoyi na dabam da basa gurbata muhalli.

Achim Steiner, Babban Daraktan Hukumar kare muhalli ta Majalisar, yace ana ci gaba da mayar da hankali wajen anfani da wannan ingantacciyar hanyar samar da makamashi a kasashe masu tasowa wanda hakan babbar nasara ce ga duniya.

Rahotan yace kasashen China da Indiya ke jagoranci a wanann fanni, inda kowanne daga cikin su ya kashe makudan kudade wajen samar da makamashin.

Rahotan yace duk da faduwar farashin mai, sabuwar hanyar samar da makamshin na cigaba da habaka, wanda hakan ya zarce anfani da gas da kuma gawayi sama da kashi 100.
Rahotan Majalisar yace wannan shine irin sa na farko a duniya
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.