Isa ga babban shafi
MDD

Sama da mutane 10.000 sun hallaka a teku a shekaru 2

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu 10 ne suka rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turai daga shekara ta 2014 zuwa yau.

Jami'an agaji na kwashe gawawakin bakin haure daga teku a Libya
Jami'an agaji na kwashe gawawakin bakin haure daga teku a Libya STRINGER / AFP
Talla

Mai Magana da yawun hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Adrian Edwards, ya ce mutane dubu uku da 500 ne suka mutu a tekun Mediterranean a 2014, sai wasu dubu uku da 771 da suka mutu a bara, yayin da wasu dubu biyu da 814 suka mutu a bana.

Yake yake ya tilastawa dubban mutane tserewa daga kasashensu na asali zuwa Turai ta teku, tafiyar da ta yi sanadiyar mutuwar daruruwam mutane sakamakon hadduran dake tattare da tafiyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.