Isa ga babban shafi
Tanzania

An Kammala Taro Na Kwanaki 4 Na Duniya Don Kare Mutuncin Mutane Zabiya

A yau littini ake kammala wani taro na kasa-da-kasa a Tanzania inda mahalarta ke duba irin matsalolin da mutane zabiya ke fuskanta a duniya.

Wata zabiya da aka datse mata hannu tana jinya a kukatwa, kasar Tanzania
Wata zabiya da aka datse mata hannu tana jinya a kukatwa, kasar Tanzania Under the same Sun
Talla

Taron,  karkashin inuwar Majalisar Dunkin Duniya  ya sami halarcin masana da kungiyoyin dake kare ‘yancin zabiya a sassan duniya.

Yayin taron na kwanaki hudu mahalarta sun nemi a kirkiro gasa don girmama darajar zabiya da kuma bullo da hukunci mai tsanani don hukunta masu amfani da zabiya don wasu ayyukan tsafi.

Mahalarta taron na cewa matsalolin da zabiya ke fama dasu a nahiyar Africa sun fi na koina tsanani, musamman a kasar Tanzania wanda hakan ne yasa aka zabi Tanzania domin wannan taro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.