Isa ga babban shafi
Tanzania

Kungiyoyin mata na fada da dokar Tanzania

Kungiyoyi mata masu gwagwarmaya a kasar Tanzania sun bukaci gwamnatin kasar da ta bai wa 'yara mata wadanda basu da aure amma suka samu juna biyu damar ci gaba da karatu, wannan kiran ya biyo bayan yadda hukumomin kasar ke korar duk macen da aka samu da ciki ba tare da aure ba daga makarantun kasar.

Wasu matan Tanzania goye da 'ya 'yansu
Wasu matan Tanzania goye da 'ya 'yansu PHOTO/MILLIYET DAILY HANDOUT/BUNYAMIN AYGUN
Talla

Doka ce a kasar Tanzania a hana mace ci gaba da karatu in har hukumomin kasar suka gano tana dauke da ciki ba tare da mijin aure ba abinda yanzu haka ya sa ake da dubun dubatan mata da suka gagara kammala karatunsu saboda wannan doka da gwamnatin kasar da ta aiwatar tun a shekara ta 2002.

Sai dai yanzu akwai alamun za a yi wa wannan dokar kwaskwarima ganin yadda mahukuntar kasar ke shirya aiwatar da wasu sauye sauyen da aka ce za su bai wa matan damar komawa su yi karatunsu da zarar sun haihu, kuma akwai matakin hukunta duk wanda aka samu da laifin yi wa yarinya da shekarunta basu kai 18 ciki ba

Kungiyoyin mata masu gwagwarmaryar 'yanci 'ya mace ne suka fito suka kaddamar da wannan campaign na ganin gwamnati ta duba ta kuma gyara wannan dokar da suka ce ta matukar haifar da tsaiko a ilimin mata a kasar.

Kasar Tanzania na sahun gaba a cikin kasashen duniya da ke da yawan yara mata masu shekaru 15 zuwa 19  da suke da ciki ko suka haihu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.