Isa ga babban shafi
Tanzania

John Pombe Magufuli ya lashe babban zaben kasar Tanzania

An tabbatar da John Pombe Magufuli a matsayin wanda ya lashe babban zaben kasar Tanzania, bayan da Hukumar zaben kasar ta fitar da sakamakon zaben da aka gudanar karshen makon da ya gabata.

John Magufuli na Jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM)
John Magufuli na Jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM) REUTERS/Sadi Said
Talla

Dan shekaru 54, John Pombe Magufuli, ya lashe wannan zabe ne bayan kidayan kuri’u, a wannan rana da ta zo dai-dai da ranar da aka haife shi.

John ya kasance malamin makaranta da ya ci zaben a karkashin Jam’iyyar da ke mulkin kasar Chama Cha Mapinduzi, CCM a takaice, Jam’iyyar da ke mulki tun shekara ta 1977, a lokacin da Jam’iyyu biyu masu zaman kansu suka dunkule wuri guda.

Yayin da wannan Jam’iyya ke murnar samun kujeran Shugaban kasa, wasu Ministocin kasar da daman na cizon yatsa saboda gaza samun nasarar kujerunsu a mazabunsu, alamarin da ke nuna sunyi bankwana kenan da mukamin Ministan.

Har ya zuwa wannan lokaci dai ana iya cewa ana zaman dar-dar saboda soke zaben yankin Zanzibar, da aka yi saboda, abinda aka kira kura-kurai a katunan zaben.

Shugaban Hukumar zaben kasar Damain Lubuva ya sanar da nasarar sabon shugaban da kuma na mataimakinsa Samia Suluhu Hassan maccen da aka ce za ta kasance ta farko a matsayin mataimakiyar Shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.