Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Ana karancin rigakafin Zazzabin cizon sauro a Congo

Gwamnatin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo na fama da karancin maganin rigakafin cutar zazzabin cizon Sauro da aka bayyana a matsayin annoba a kasar. Sauro ne ke yada cutar da ake kira Yellow Fever mai kama da zazzabin Zika.

Nau'in Sauron da ke yada Zika ne ke yada Cutar Yellow Fever
Nau'in Sauron da ke yada Zika ne ke yada Cutar Yellow Fever
Talla

Minsitan lafiya Felix Kabange ya ce yanzu haka an samu wadanda suka kamu da cutar 67 a Kinshasa, da Tsakiyar Congo da kuma Kwango yayin da ake sa ido kan wasu mutane sama da 1,000.

Gwamnatin kasar tare da hukumar lafiya ta duniya sun yi wa mutane sama da miliyan biyu rigakafi tsakanin watan Mayu zuwa 4 ga watan nan.

Cutar dai ta tsallaka Congo ne daga Angola, kuma hukumar Lafiya ta duniya tace yanzu cutar ta shiga Kenya da kuma China.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.