Machar ya tube wani ministan Sudan ta kudu
Shugaban ‘Yan tawayen Sudan ta kudu Riek Machar ya tube wani minista daga mukaminshi bayan zargin gwamnarin Salva Kiir na yunkurin nada shi mataimakin shugaban kasa.
Wallafawa ranar:
Machar ya tube ministan ne na albarkarun kasa mai suna Taban Deng Gai tsohon kwamandan ‘yan tawaye wanda ya jagoranci tattaunawar sulhu da bangaren gwamnatin Salva Kiir.
Machar ya gargadi Salva Kiir cewar tube shi daga mukamin mataimakin shugaban kasa zai wargaza gwamnatin hadaka da yarjejeniyar sulhu da suka amince a watan Agustan 2015.
Tuni dai Salva Kiir ya lallashi Machar ya dawo Juba domin aiki tare wajen sasanta juna.
Sai dai kuma ‘Yan tawayen na zargin Salva Kiir da kokarin halaka Riek Machar.
Sama da mutane 300 aka kashe a sabon rikicin da ya barke a farkon watan Yuli tsakanin dakarun Salva Kiir da na Riek Machar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu