'Yan sanda Malawi sun cafke mutumin da ya sadu da 'yan mata 100
A kasar Malawi, ‘Yansanda sun kama mutumin nan da ke dauke da kwayar cutar HIV kuma ya sadu da ‘yan mata sama da 100 da sunnan al’adar, bayan an biya shi kudi.
Wallafawa ranar:
An gurfanar da Mutumin mai suna Eric Aniva a gaban kotu bisa laifin cin zarafin yara kanana da kuma zargin yada cutar HIV a kasar.
Mista Aniva da ya sadu da ‘yan mata sama da 100, ya ce ya yi hakan ne bisa umarnin iyayen ‘yan matan dake biyansa kudi, don saduwa dasu da sunan al’adar tsarkake ‘ya’yan nasu kamar yadda yake a al’adar al’ummar yankin kudancin kasar ta Malawi
Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika ne dai ya bayar da umarnin kama Mista Aniva bayan kafaffen yada labaran kasar sun dauki labarin yadda ake biyanshi kwatakwacin dalar Amurka hudu ko bakwai don yin Jima’I da kowacce mace guda, shugaba Mutharika ya bukaci gudanar da bincike ga rawar da iyalan ‘yan matan suka taka tare da tantance lafiyarsu
Gwamnatin Malawi ta dadde tana adawa da wannan al’ada inda yanzu haka ta bukaci wargazata baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu