Isa ga babban shafi
Malawi

Malawi za ta haramta auren yara kanana

Gwamnatin Kasar Malawi na shirin amincewa da wata dokar da zata hana aure da wuri har sai ma’auratan sun kai shekaru 18, bayan Majalisar kasar ta amince da dokar a makon jiya. Dokar na dauke da hukuncin daurin shekaru 10 ga dukkan wanda ya saba wa dokar.

Shugaban Malawi Peter Mutharika
Shugaban Malawi Peter Mutharika AFP PHOTO / AMOS GUMULIRA
Talla

Kasar Malawi na daya daga cikin kasashen da ake yawan auren yara kanana, inda ake aurar da masu shekaru 9 zuwa 10 kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito.

Nan da makwanni uku ake sa ran Shugaban kasar Peter Mutharika zai sanya hannu kan amincewa da dokar.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce kimanin mata ‘yan kasa da shekaru 18 Miliyan 15 ake aurar wa duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.