Isa ga babban shafi
Najeriya

Avengers sun yi barazanar ballewar Naija Delta daga Najeriya

Kungiyar tsagerun Naija Delta da ke kira Avengers ta yi barazanar ballewar yankin kudancin kasar mai arzikin fetir daga Najeriya tana mai zargin shugaba Muhammadu Buhari da rarraba kan al’ummar kasar.

Tsagerun Avengers a Naija Delta sun bulla ne a Najeriya bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari
Tsagerun Avengers a Naija Delta sun bulla ne a Najeriya bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari via pulse
Talla

Kungiyar ta fitar da sanarwar ne a jiya Alhamis kwana guda bayan ta bayyana aniyar tattaunawa da gwamnati.

A cikin sanarwar kungiyar ta soki gwamnatin Buhari ta gazawa tare da raba kan ‘yan Najeriya.

Kungiyar ta koka kan yadda manufofin gwamnati mai ci ke rarraba kan ‘Yan Najeriya wanda ya kai ga mutanen kasar da dama ba su bukatar ci gaba da zama ‘Yan kasar.

Kungiyar ta bayyana shirin ballewa daga Najeriya da kuma kafa kasa mai cin gashin kanta daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

Tun hawan Buhari kan karagar mulki Tsagerun na Naija Delta suka kaddamar da hare hare kan bututun mai da kadarorin gwamnati a kudancin Najeriya mai arzikin fetir.

Yanzu haka kuma jaridun Najeriya sun ruwaito cewa gwamnatin Buhari ta kaddamar da bincike akan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ake zargi yana cikin wadanda ke daukar nauyin tsagerun na Naija Delta bayan ya sha kaye a zaben 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.