Isa ga babban shafi
Afrika

Japan zata tallafawa Afirka da Dala Biliyan 30

Gwamnatin kasar Japan tace zata tallafawa kasashen Afirka da agajin Dala biliyan 30 a cikin shekaru uku masu zuwa, wajen ganin sun gina kayan more rayuwa, bunkasa ilimi da kula da lafiyar al’umma.

Firaministan kasar Japan Shinzo Abe
Firaministan kasar Japan Shinzo Abe Reuters
Talla

Firaministan Kasar Shinzo Ane ya bayyana haka a taron hadin gwuiwa tsakanin shugabanin kasashen Afirka 30 da jami’an gwamnatin Japan da ake gudanarwa a Nairobi, inda yake cewa Japan na da sha’awar ma’adinan da Allah ya wadata Afirka da su.

Abe yace an samu karuwar cinikayyan mannfetur da iskar gas bayan hadarin da aka samu a tashar nukiliyar Fukushima.

Firaministan yace za’a kasa tallafin na dala biliyan 30 cikin shekaru uku, kuma da taimakon Bankin Afirka wanda zai taka rawa wajen sa ido kan yadda za’a kashe kudaden.

Wannan tallafi na Dala biliyan 30 ya sha bam bam da na Dala biliyan 32 da Japan ta yiwa Afirka alkawari a shekarar 2013.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.