Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Shugaban Burkina Faso ya umurci Isaac Zida da ya dawo gida

Janar Isaac Zida tsohon Firaministan kasar Burkina Faso dake zaune a kasar Canada tun bayan  hawan sabon Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore na fuskantar tuhuma daga hukumomin kasar sa.Shugaban kasar, Kabore ya  shigar da wasika zuwa babban hafsan sojan kasar na ganin an tube Janar  Isaac Zida dama bayyana gaban alkalai. 

Tsohon Firaministan Burkina Faso Janar Isaac Zida
Tsohon Firaministan Burkina Faso Janar Isaac Zida AFP PHOTO
Talla

Rahotanni daga Burkina Faso na nuni cewa Janar Zida ya samu izini futa daga kasar Burkina bayan da shugaban wucin gadi na lokacin Shugaba Kabore ya sanya hannu a takardar izini a watan Disemba na shekara ta 2015.

Ranar 15 gawatan fabrairu shekarar nan ta 2016 ne ya dace ya dawo kasar ta Burkina,ki kasancewa  a cikin kasar ya zuwa yanzu a cewar fadar shugaban kasar bai dace ba,sabili da haka ya dace hukumomin kasar su dau matakan da suka dace a kai.

Za a kaddamar da bicinke kan tsohon Firaministan Burkina Faso Janar Isaac Zida wanda nan take Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ya kaffa comity na musamman.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.