Isa ga babban shafi
Congo

Jami'an tsaro sun halaka fararen hula 48 a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce jami’an tsaron kasar Congo, sun halaka fararen hula 48 ta hanyar harbi, duka, da kuma azabtarwa ta hanyar kona su, yayin da suke gudanar zangar zangar adawa da tazarcen Shugaban kasar Joseph Kabila.

Zanga zangar adawa da gwamnatin Joseph Kabila a Congo Brazaveille
Zanga zangar adawa da gwamnatin Joseph Kabila a Congo Brazaveille
Talla

Rahoton Majalisar dinkin Duniyar ya ce rasa rayukan mutanen, ya biyo bayan rikicin da ya barke tsawon kwanaki biyu a birnin Kinshasa a watan da ya gabata.

Yayin da yake jawabi kan rahoton, mai bawa shugaba Kabila Shawara kan huldar Diplomasiya, Barnabe Kikaya, ya amince da cewa jami’an tsaron kasar, sun aikata laifukan, sai dai ya ce, sun yi hakan ne domin tsaron lafiyarsu, a cewarsa mutanen ne suka fara farwa jami'an tsaron.

Sai dai kuma Kikaya ya musanta cewa jami’an tsaron, ga gangan suka bude wuta kan masu zanga zanga a satin da ya gabata, inda akalla mutane 32 suka mutu.

A ranar 19 ga watan Satumba da ya gabata, gamamyyar jam’iyyun adawar kasar Congo. suka yi kira da a gudanar da zanga zanga, don tilastawa Joseph Kabila sauka daga shugabancin kasar wanda yake kai tun a shekarar 2001.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.