Isa ga babban shafi
Faransa

An kama wasu yan kasar Congo Brazzaville a Paris

Hukumomin Faransa sun sanar a jiya da kama wasu yan kasar Congo Brazzaville takwas, mutanen kamar dai yada rahotani suka tabbatar sun yi kutse ne cikin ofishin jakadancin kasar dake Paris ,wata hanyar nuna adawar su da yunkuri shugaban kasar Denis Sassoun Nguesso na neman yiwa kudin tsarin mulkin kasar gyara.

Denis Sassou Nguesso Shugaban kasar Congo Brazzaville
Denis Sassou Nguesso Shugaban kasar Congo Brazzaville AFP/Thierry Carlier
Talla

Yan adawa a kasar dama wasu kungiyoyin fararen fula na ci gaba da yi tir da allah wadai kan wanan shirin na shugaban kasar Denis Sassou Nguesso mai shekaru 72 a Duniya,wanda kuma ya kwashe akala shekaru 30 a karagar mulkin kasar, al’amarin da ya sabawa kudin tsarin mulki kasar.

Ya zuwa yanzu hukumomin Faransa ba su ce upon ba dangane da wannan yamuci a ofishin jakadancin Congo Brazzaville dake birni Paris .

To sai dai masu hamayya da shi a fagen siyasa sun nuna rashin amincewarsu da hakan, yayin da alamu ke nuni da cewa akwai yiyuwar a samu tarzomar nuna adawa da hakan akan titunan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.