Isa ga babban shafi
Kenya

Kenya za ta jinkirta rufe sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab

Gwamnatin kasar Kenya ta amince ta kara wa’adin watanni shida kafin ta kai ga rufe sansanin Dadaab na ‘yan gudun mafi girma a Duniya.

'Yan gudun hijra fiye da dubu dari biyu ke rayuwa a sansanin Dadaab.
'Yan gudun hijra fiye da dubu dari biyu ke rayuwa a sansanin Dadaab. TONY KARUMBA / AFP
Talla

A baya gwamnatin Kenya ta ce tilas ne ta rufe sansanin saboda zargin mayakan El-Shabab da ta ce na amfani da sansanin wajen kai mata hare-haren ta’addanci, kafin daga bisani ta dakatar da yunkurin bayan matsin lambar da ta fuskanta daga kasashen duniya.

Kungiyoyin kare hakkin dan’adam sun soki matakin sansanin bisa cewar hakan zai sake jefa ‘yan gudun hijirar da suka gujewa tashin hankali a Somalia cikin tsanani na rasa inda za su dosa.

Yawancin 'Yan gudun hijrar da ke sansanin 'yan asalin kasar Somaliya ne da yaki ya tilastawa barin kasar.

Sansanin na tsugune da 'yan gudun hijira fiye da dubu dari biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.