Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Ban Ki-moon ya bukaci kawo karshen rikici a Afrika ta Tsakiya
Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nemi bangarorin da ke yakar juna a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika da su kawo karshen fadan da ke salwantar da rayukan al’ummar kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Babban Sakataren ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa inda ya ce dukkan kungiyoyi dake dauke da makamai ya zama tilas su ajiye makamai su kuma rungumi zaman lafiya da juna.
Rikicin kasar dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da tamanin da biyar, yayin da wasu dubu goma sha daya suka rasa matsuguni
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu