Isa ga babban shafi
Ghana

'Yan adawa sun yi ikirarin lashe zaben Ghana

Babbar jam’iyyar adawa ta Ghana ta yi ikirarin lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a jiya, yayin da ta bukaci shugaba Dramani Mahama da ya amince da shan kayi.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama  da abokin hamayyarsa and Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama da abokin hamayyarsa and Nana Akufo-Addo AFP/Wikimedia CC
Talla

Jam’iyyar ta NPP ta bayyana cewa, dan takararta Nana Akufo-Addo ya lashe kashi 52 cikin 100 a lissafin da ta yi a jiya Laraba, abin da ke nuna cewa Mahama na da kashi 44.8.

Shugaban yakin neman zaben jam’iyyar, Peter Mac Manu ya ce, sun tattara alkalumansu ne a rumfunan da aka kada kuri’u.

Sai dai hukumar zaben kasar ta ce, kawo yanzu, ba ta fitar da wani sakamako.

Rahotannin da kafofin talabijin da rediyo na kasar suka fitar, sun nuna cewa, ‘yan adawar na samun rinjaye a zaben na shugaban kasa da na ‘yan majalisu.

Wani lokaci a yau ne ake sa ran fitar da sakamakon zaben a hukumance.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.