Isa ga babban shafi
Kamaru

Amnesty International ta bukaci a binciki amfani da karfi kan farar hula a Kamaru

Kungiyar kare hakkin dan’adam ta Amnesty international, ta ce dole gwamnatin kasar Kamaru ta gudanar da bincike kan zargin da amfani da karfi fiye da kima kan fararen hula a garin Bamenda, da ‘yan sanda suka yi tare da hukunta jami’an da aka samu da laifi.

Masu zanga zanga a garin Bamenda, Kasar Kamaru
Masu zanga zanga a garin Bamenda, Kasar Kamaru Via social media, independently verified.
Talla

Jama'ar garin Bamenda na amfani da harshen turanci maimakon na Faransanci da mafi yawan kasar ke amfani da shi.

Rahotanni sun ce akalla mutane 4 ne suka rasa ransu yayin da jama’ar garin ke zanga zangar adawa da gwamnatin kasar, don neman bukatar basu damar amfani da yaren da suke so, hadi da basu kulawar da ta kamata, sakamakon bude musu wuta da jami’an tsaro suka yi.

Sai dai kuma a martaninta wata majiya daga rundunar ‘yan sandan kasar ta ce, jami’an sun yi amfani da karfi ne kasancewar masu zanga zangar na dauke da makamai.

Mazauna garin na zargin gwamnatin Kamaru da nuna fifiko kan yankunan da ke amfani da harshen Faransanci.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.