Isa ga babban shafi
Gambia

MDD ta bukaci Jammeh dole ya sauka

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zama dole ga shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya sauka daga kujerar sa ranar 19 ga watan Janairu mai zuwa da zaran wa’adin sa ya kare ranar 18 ga wata.

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh
Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Jakadan Majalisar a Afirka ta Yamma, Muhammad ibn Chambas, ya bayyana haka inda yake cewa babu wani dalili da Jammeh zai ci gaba da jagorancin Gambia bayan ya fadi zabe kuma duniya ta gani.

Chambers ya ce lalle za’a dauki mataki mai karfi kan shugaban mai barin gado muddin ya zarce ranar 18 ga watan Janairu akan karagar mulki.

Jami’in na Majalisar Dinkin Duniya bai ce komai ba kan daukar matakan soji dan kauda shugaban, amma ya ce suna duba yiwuwar daukar matakan da suka dace dan ganin an magance rikicin cikin ruwan sanyi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.