Isa ga babban shafi
Gambia

ECOWAS ta bukaci Jammeh ya mika mulkin Gambia

Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika sun bukaci gaggauta kawo karshen rikicin siyasar Gambia, bayan Yahya Jammeh ya ki amincewa da shan kayi a zaben shugabancin kasar da Adama Barrow ya lashe.

Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika a birnin Abuja na Najeriya
Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika a birnin Abuja na Najeriya RFI hausa
Talla

Shugabannin sun bukaci haka ne a taron ECOWAS na 50  da suka gudanar a birnin Abuja na Najeriya, in da suka mafi mayar da hankali kan rikicin siyasar Gambia.

Tuni dai Jammeh ya shigar da kara a kotun koli don kalubalantar sakamakon wanda ya amice da shi a farko kafin ya bijire daga bisani.

A farkon makwannan ne dakarun Jammeh suka kwace hukumar zaben kasar, abin da ya janyo masa suka daga kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.