Isa ga babban shafi
ECOWAS-GAMBIA

ECOWAS na cikin shirin ko-ta-kwana domin kawar da Jammeh

Dakarun kungiyar kasashen yammacin Afirka na cikin shirin ko-ta-kwana domin kawar da Yahaya Jammeh na Gambia daga mulki muddin yaki mika mulki idan wa’adinsa ya cika a ranar 19 ga watan Janairu.

Yayha Jammeh na Fuskantar Matsin lambar ya mika mulki
Yayha Jammeh na Fuskantar Matsin lambar ya mika mulki REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Marcel de Souza, ya ce sun jibge jami’an tsaron ne da Senegal ke jagoranci, domin ba za su zura ido a danne hakkin mutane a kasar ba

Jammeh da bai tanka wannan batu ba, a baya ya ce Ecowas bata da ikon tsoma baki kan harkokin cikin gida Gambia.

Sai dai suma gamayar ‘yan adawar kasar sun lashi takobin gani lallai an rantsar da zabebben shugaba Adama Barrow a watan gobe.

A cewar ‘yan adawa ba zasu saurare hukunci kotu ba, kuma tabbas Barrow na da kwarin-gwiwar shi ya lashe zabe, don haka babu wata kotu a duniya da za ta yanke hukunci sabanni haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.