An gano gawarwakin mutane 74 a gabar teku
Kungiyar Agaji ta Red Crescent tace an gano gawarwakin wasu baki 74 da suka mutu a tekun meditareniyan yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa nahiyar Turai daga Libya.
Wallafawa ranar:
Kungiyar tace mazauna kauyen Harcha dake wajen garin Zawiya mai nisan kilomita 45 daga Tripoli suka shaidawa masu aikin agaji gano gawarwakin, bayan ruwan ya turo su gabar teku.
Kungiyar dake sa ido kan baki tace ranar lahadi wani kwale kwalen mai dauke da mutane kusan 100 ya kife a takun na Meditareniyan.
Kakakin hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta duniya IOM, Flavio Di Giacomo ya ce, binciken da suka gudanar ya nuna cewa, an bar kwale kwalen robar dauke da bakin, yana watangaririya a kan teku tsawon kwanaki bayan lalacewar injinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu