Isa ga babban shafi
Libya

Libya ta taso keyar ‘Yan Najeriya 159

Mahukuntan kasar Libya sun taso keyar ‘yan Najeriya 159 zuwa gida a yau Alhamis bayan da aka kama su suna kokarin tsallakawa zuwa Turai, wannan ne karo na biyu da aka dawo da ‘yan ci-ranin na Najeriyar a mako guda.

Libya na taso keyar 'Yan Afrika da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai
Libya na taso keyar 'Yan Afrika da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Shugaban hukumar kula da bakin haure a Libya Badredine Ben Hameed, ya ce an tasa keyar ‘yan Najeriyar ne karkashin wani hadin gwiwa tsakaninsu da hukumar kula na bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya OIM.

Akwai dai mata da dama cikin ‘yan ci-ranin da Libya ta taso keyarsu.

Wannan na zuwa bayan Libya ta taso keyar ‘yan kasar Cote d’Ivoire kimanin 150 a ranar Talata.

Kasar Libya dai ta kasance hanyar da ‘yan ci-rani ke ratsowa yawanci daga Nijar domin tsallakawa zuwa kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.