Isa ga babban shafi
Gambia

Jam’iyyar UDP ta samu rinjaye a zaben ‘yan majalisar Gambia

Jam’iyyar UDP ta shugaban kasar Gambia ta samu gagarumin rinjaye a zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a jiya alhamis, inda jam’iyyar ta samu kujeru 31 daga cikin 53.

Jam’iyyar UDP ta samu rinjaye a zaben ‘yan majalisar Gambia
Jam’iyyar UDP ta samu rinjaye a zaben ‘yan majalisar Gambia REUTERS
Talla

Jam’iyyyar tsohon shugaban kasar ta Gambia Yahya Jammeh ta samu kujeru biyar kacal ne a zaben, kuma dukanninsu a lardin Foni wanda shi ne mahaifar tsohon shugaban kasar.

Jam’iyyun adawa da dama dai sun hada kai a zaben shugaban kasar da ya kawo karshen mulkin shugaba Jammeh na shekaru 22, sai dai a wannan karon Jam’iyyun sun kama gaban su dan kowacce ta samu kujeru a zauren Majalisar.

Zaben na ‘yan majalisun ya kasance irinsa na farko tun bayan kauda shugaba Yahya Jammeh daga karagar mulki da kuma zaben Adama Barrow akan karagar mulki.

Yan kasar 880,000 suka shiga zaben da aka gudanar a jiya Alhamis.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.