Isa ga babban shafi
Togo

Togo na nazarin takaita wa’adin shugaban kasa

Majalisar zartarwar Togo ta amince da shirin sanya wa’adin shugaban kasa a cikin kundin tsarin mulkin kasar sakamakon zanga zangar da ‘yan adawa suka kaddamar.

'Yan adawa sun kaddamar da zanga-zanga a sassan Togo
'Yan adawa sun kaddamar da zanga-zanga a sassan Togo PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Daukar matakin zai bada damar gabatar da kudirin ga Majalisar dokoki domin yin doka akai.

Mutane sama da dubu dari ne suka gudanar da zanga-zanga a cikin birane 10 na kasar Togo, inda suka bukaci gwamnatin shugaba Faure Gnassingbe ta aiwatar da sauye-sauye ciki har da dawo da wa’adin shugabancin kasar sau biyu kawai.

Shugaba Faure Gnassingbe da ya hau karagar mulki a shekarar 2005 yanzu haka yana wa’adi na uku bayan ya gaji mahaifinsa da ya kwashe shekaru 38 a karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.