Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Boko Haram 45 aka daure a gidan yari

Gwamnatin Najeriya ta ce ‘yan Boko Haram 45 aka zartarwa hukuncin dauri a gidan yari tsakanin shekaru 3 zuwa 31 a shari’arsu da aka gudanar a asirce a kotu ta musamman a jihar Neja.

Ministan watsa labaran Najeriya Lai Muhammed
Ministan watsa labaran Najeriya Lai Muhammed fmi.gov.ng
Talla

Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ne ya fadi haka a cikin wata sanarwa amma ba tare da bada cikakken bayani akan sunayensu da shekaru da inda aka kama su da kuma laifukan da aka tuhume su ba.

An haramtawa ‘Yan jarida zuwa wajen Shari’ar ta ‘yan Boko Haram, wacce ita ce ta farko da aka gudanar a wani sansanin Soji da ake tsare mutane a Kainji Jihar Neja.

Daga cikin mutane 575 da ake zargi ‘yan Boko Haram ne da aka gurfanar a kotun, za a saki 468 wadanda aka gano ba su da laifi bayan sun samu horo na gyara hali, sannan za a ci gaba da tsare 28 a Abuja da Minna a Neja.

Nan gaba, gwamnati ta ce za a sake yin shari’ar wasu da ake zargi ‘yan Boko Haram da ake tsare da su a barikin Giwa a garin Maiduguri Jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.