Isa ga babban shafi
Liberia

EU ta bukaci matsin lamba ga 'yan siyasar Liberia

Kungiyar kasashen Turai ta bukaci kasashen duniya da su matsawa manyan ‘yan siyasar Liberia domin ganin an kawo karshen tankiyar da ake samu wajen kamala zaben shugaban kasar.

Dan takarar jam'iyyar adawa ta CDC a zaben shugabancin kasar Liberia George Weah, yayin kada kuri'a a babban birnin kasar Monrovia, 10 ga Oktoba, 2017.
Dan takarar jam'iyyar adawa ta CDC a zaben shugabancin kasar Liberia George Weah, yayin kada kuri'a a babban birnin kasar Monrovia, 10 ga Oktoba, 2017. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Wannan kira ya biyo bayan jinkirin da aka samu wajen kamala zaben shugaban kasar zagaye na biyu, sakamakon umurnin kotun koli na ganin hukumar zabe ta gudanar da bincike kan zargin magudi da daya daga cikin yan takarar kasar yayi.

Ita ma kungiyar kasashen Afirka ta AU da kungiyar ECOWAS, da wakilan Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci ganin an gaggauta kammala shari’ar kalubalantar zaben domin gudanar da zabe zagaye na biyu tsakanin George Weah da Joseph Boakai.

A ranar talata ne gwamnatin Ellen Johnson Sirleaf ta musanta rahotannin da ke cewa ta fara tattaunawa da jam’iyyar dan takara George Weah kan kada ya bincike wasu al’amura idan yayi nasarar zama shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.