An kashe masu zanga-zanga a Kenya
‘Yansanda a kasar Kenya sun tabbatar da mutuwar mutane biyu bayan da kotun kolin kasar ta yanke hukuncin amincewa da zaaben da aka yi wa Uhuru Kenyatta a matsayin shugaban kasa.
Wallafawa ranar:
A ranar Litini ne kotun ta sanar da matsayarta bayan sauraron korafe-korafen da aka shigar a gabanta daga bangaren ‘yanadawa.
'Yandsanda sun rinka harbi domin tarwatsa magoya bayan ‘yan'adawar kasar masu zanga-zanga a yankin Kisumu.
Mutum daya ne aka tabbatar ya halaka a unguwar marasa galihu ta Kibera da ke birnin Nairobi, yayin da aka harbe wani a yammacin yankin Migori.
A bangare daya kuma, kade-kade da raye-raye ne suka barke, musamman ma a tsakanin magoya bayan shugaba Uhuru Kenyatta, wanda kotu ta bai wa nasara.
A ranar Litini ne kotu ta bayyana cewa korafe-korafen da aka shigar gabanta na neman soke zaben ba su da kwari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu