Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia ta yi bikin cika shekaru 53 da samun 'yanci

Al’umar Gambia sun gundanar da bukukuwa biyu a jiya lahadi, wato cikar kasar shekaru 53 da samun ‘yancin-kai da kuma na shekara daya da rantsar da Adama Barrow a matsayin shugaban kasar.

Al'ummar Gambia na murnar cika shakaru 53 da samun 'yancin-kai da kuma cikar Adama Barrow shekara guda kan karagar mulkin kasar
Al'ummar Gambia na murnar cika shakaru 53 da samun 'yancin-kai da kuma cikar Adama Barrow shekara guda kan karagar mulkin kasar RFI/Claire Bargelès
Talla

Gambia dai ta samu ‘yancin-kai ne a ranar 18 ga watan fabarairun 1965, abin da ke nufin cewa kasar ta cika shekaru 53 da samun ‘yanci daga Ingila.

To sai dai wani abu dangane da wannan rana, shi ne yadda bara warahaka aka rantsar da Adama Barrow a matsayin shugaba, bayan kawo karshen mulkin shekaru 22 na shugaba Yahya Jammeh.

Duk da cewa a karkashin dokokin kasar ta Gambia ana zaben shugaba ne domin yin wa’adin mulki na shekaru biyar cur, to sai dai Adama Barrow ya kulla kawance da sauran jam’iyyun siyasa na kasar domin yin wa’adin shekaru uku kacal.

Yanzu haka dai akwai alamun da ke nuni da cewa an fara samun bambancin ra’ayoyi a tsakanin al’ummar kasar, musamman tsakanin masu goyon bayan yarjejeniyar da kuma wadanda ke ganin cewa ya zaman wajibi a mutunta kundin tsarin mulkin kasar da ke cewa ana tafiyar da mulkin kasar ne shekaru biyar amma ba 3 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.