Najeriya
An cafke matashi da ke damfarar jama'a da sunan Sarkin Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 20 bisa laifin damfarar mutane kudade ta hanyar amfani da sunan Sarkin Kano Muhammdu Sanusi na II a shafin sada zumunta na Instagram.
Wallafawa ranar:
Talla
Kakakin Rundunar DSP Magaji Musa Majiya ya ce, yanzu haka suna kan gudanar da bincike kan matashin mai suna Sultan Bello, kafin mika shi ga kotu don fuskantar hukunci.
Matashin ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya karbi dimbi kudade daga jama’a da sunan Sarkin na Kano kafin dubunsa ta cika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu