Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An yi wa Winnie Mandela addu'o'i a Afrika ta Kudu

An kwashe tsawon jiya Laraba ana gudanar da adduoi na musamman ga marigayiya Winnie Mandela, tsohuwar mai dakin marigayi Nelson Mandela, yayin da ake shirin jana'izarta a ranar Asabar a Afrika ta Kudu.

Marigayiya Winnie Mandela.
Marigayiya Winnie Mandela. AFP/Odd Andersen
Talla

Dubban jama’a ne dai suka halarci addu'o'in da aka yi a filin wasanni na Orlando da ke Soweto, in da suka yi ta wakokin jinjina ga Winnie Mandela wadda ta taka rawar gani wajen yakar mulkin wariyar launin fata a kasar.

Da dama daga cikin mahalarta addu'o'in sun musanta bayanan da ke alakanta marigayiyar da cin zarafin mutane a wasu lokuta a rayuwarta, abin da suka ce farfaganda ne kawai don bata ma ta suna.

Wasu kuwa cewa suka yi, uwargida Winnie ta bar mu su darussa da yawa da za su dauki tsawon lokaci suna cin moriyarsu.

A ranar Asabar ne dai za a yi ma ta karramawa ta karshe da addu'oi a Soweto.

Gwamnatin Afrika ta Kudu dai ta sanar da zaman makoki na tsawon kwanaki 10  da za a kammala a ranar Asabar bayan binne gawarta a makabartar tuna wadanda suka yi wa kasar gwagwarmaya a  birnin Johannesbourg.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.