Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta haramta kiwo a wasu jihohin kasar biyar

Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin hana makiyaya yawon kiwo a Jihohi 5 da suka hada da Benue da Taraba da Nasarawa da Kaduna da kuma jihar Adamawa.Matakin ya biyo bayan tashin hankalin da ke haifar da kashe kashe da asarar rayuka a wadanna Jihohi.

Matakin dai a cewar gwamnati na da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fuskanta tsakanin Makiyayan da Manoma.
Matakin dai a cewar gwamnati na da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fuskanta tsakanin Makiyayan da Manoma. guardian.ng
Talla

Bayan wani zama da majalisar zartaswar Najeriyar ta gudanar karkashin jagorancin Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo tare da ilahirin gwamnonin kasar da wasu daga cikin ministoci, sun amince da daukar matakin haramta kiwon a wasu daga cikin jihohin kasar.

Osinbajo ya shaidawa maneman labaran fadar shugaban kasa cewa nan ba da jimawa ba dokar za ta fara aiki yayinda za a tanadar da wuraren kiwo ga dimbin makiyayan da ke jihohin 5.

A cewarsa ta hakan ne kadai za a kawo karshen rikice-rikicen da ake samu tsakanin Makiyaya da Manoma a kasar wanda a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.