Isa ga babban shafi
Najeriya

Fursunoni 219 sun tsere daga Yari a Najeriya

Rahotanni daga Jihar Niger da ke Najeriya sun ce akalla yan gidan kaso sama da 200 suka tsere daga gidan yarin garin daren jiya, bayan da wasu dauke da makamai suka kai hari gidan yarin da misalign karfe 8 na dare.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake fuskantar ballewar fursunoni daga Yari a jihar ta Nija ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake fuskantar ballewar fursunoni daga Yari a jihar ta Nija ba. NAN
Talla

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Dibal Yakadi ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya ce an kama 19 daga cikin yan gidan kason 219 da suka tsere.

Tuni dai rundunar da ke bayar da tsaron gidan yarin ta tabbatar da mutuwar guda cikin jami’insu wanda ya yi kokarin tare wasu daga cikin ‘yan yarin, a daren jiya Lahadi.

Kamfanin dillacin Labaran Najeriyar ya ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga ne suka shirya lamarin inda suka balle gidan yarin da ke yankin Tunga a tsakiyar birnin Minna.

Haka zalika cikin wadanda suka mutu a kokarin balle gidanb yarin har da wani mai mashin da ya zo giftawa ta wajn da abin ke faruwa.

Rundunar ‘yansandan jihar ta ce tuni ta kafa kwamiti na musamman don binciken wadanda ke da hannu a harin da ya kai ga guduwar akalla fursunoni 200.

A cewar rundunar da zarar an gano wadanda ke da hannu babu shakka za a hukunta su don zamowa izina ga na baya.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake fuskantar ballewar fursunoni daga Yari a jihar ta Nija ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.