Isa ga babban shafi

Jean-Pierre Bemba zai koma gida gabannin babban zabe

Jam’iyyar tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, Jean-Pierre Bemba, tace jagoran nasu zai koma gida ranar 1 ga watan Agusta domin tsayawa takarar zaben da za’ayi a karshen wannan shekara.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba. REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Wata sanarwar da Jam’iyyar at rabawa manema labarai na dauke da cewar, bayan shekaru 10, shugaban su Sanata Jean-Pierre Bemba Gomba zai koma Congo, kasar kakannin sa ranar 1 ga watan Agusta.

Jam’iyyar ta bukaci magoya bayan su da su fitar farin dango domin tarbar shugaban wanda kotun hukunta manyan laifufuka ta wanke.

A farkon watan Yuli na wannan shekara ce jam’iyyar adawa da MLC, ta zabi kasar Jean Pierre Bemba, a matsayin dan takarar ta, a zaben shugabancin kasar, makwanni kadan bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta wanke shi daga zargin aikata laifukan yaki a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Takarar dai ka ‘iya zama babban kalubale ga gwamnatin shugaba Joseph Kabila, wanda ‘yan adawa ke zargin yana da aniyar sake tsayawa takara a zaben kasar na watan Disamba mai zuwa, bayan kin sauka daga mukaminsa da ya yi, duk kuwa da cewa wa’adinsa ya kare tun a shekarar da ta gabata.

Kin saukar Kabila da ke shugabantar Jamhuriyar Congo tun daga shekarar 2001 ya haddasa jerin zanga-zanga a kasar, da sukai sanadin hallakar rayukan 'yan kasar da dama da ke neman tilastawa shugaban yin murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.