Isa ga babban shafi
Nijar

Mutane 36 suka mutu sakamakon ambaliya ruwa a Nijar

Majalisar dinkin Duniya ta ce akalla mutane 36 ne aka tabbatar da mutuwar su a Jamhuriyar Nijar sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a watan yuni,kuma akasarin su sun fito ne daga yankin arewacin kasar.

Wasu yankuna kasar Nijar da aka samu ambaliya
Wasu yankuna kasar Nijar da aka samu ambaliya RFIHAUSA/Awwal
Talla

Hukumar jinkai ta majalisar dinkin Duniya da ake kira OCHA ta bayyana cewa a watan yuni,mutane 130.468 ambaliyar ta shafa,inda ta lalata gidaje 7.212 da eka 8.162 na gonaki da kuma hallaka shanu 31.118.

Alkaluman hukumar sun ce ambaliyar tafi ta'adi a jihar Agadez,cibiyar kasuwanci da kuma zangon matafiya,inda ta shafi mutane 60.555.

Wasu yankunan da matalar ta shafa sun hada da Maradi,da Zinder da kuma Diffa.

Majalisar dinkin Duniya ta ce a bara mutane kusan 20 suka mutu a birnin Yameh,sakamakon ambaliyar da aka samu daga cikin mutane 56 da suka mutu sakamakon ambaliyar da ta shafi mutane 206.000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.