Nijar
Boko Haram na ci gaba da garkuwa da mutane 39 na Ngalewa
A kwana a tashi kwanaki 500 kenan cur, da mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da mutane 39 da suka hada da mata da kananan yara a garin Ngalewa da ke jihar Diffa a Jamhriyar Nijar.
Wallafawa ranar:
Talla
Iyalai da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama a kasar ta Nijar, sun bayyana damuwarsu dangane da yadda har yanzu mahukuntan kasar suka kasa ceto wadannan mutane.
Rashin ceto mutanen na ci gaba da haifar da fargaba a yankin inda masu fafutukar ganin an ceto su suka shigar da kokensu zuwa hukumomin kasar ta Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu