Gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da tsawaita dokar ta bacin da ta kaddamar a yankin Diffa saboda ci gaba da barazanar tsaron da ake fuskanta a yankin.
Wallafawa ranar:
Sanarwar gwamnatin ya nuna cewar an tsawaita dokar ne daga yau 18 ga watan Satumba zuwa watanni 3 nan gaba.
Zalika tawaita dokar ya shafi yankin dake makwabtaka da Mali inda ake samun hare hare a Tilaberi da Tawha.
To sai dai a nasu bangaren wasu daga cikin mazauna yankunan da matakin ya shafa sun ce zai yi wahala matakin tsawaita dokar ta bacin ya yi tasiri wajen magance barazanar tsaron, kamar yadda wani mazauni a yankin na Diffa AbdouSalam Djamal ya shaidawa sashin Hausa na RFI.
Gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu