Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Fiye da Fasinjojin mota 42 sun kone kurmus a Zimbabwe

Jami'an tsaro a Zimbabwe sun tabbatar da gano gawar akalla mutane 42 da suka rasa rayukansu sanadiyyar konewar motar da su ke ciki gab da birnin Bulawayo.

Sai dai jami'an tsaron sun ce akwai wasu Fasinjoji da suka samu raunuka wadanda yanzu haka su ke karbar kulawar gaggawa a Asibiti.
Sai dai jami'an tsaron sun ce akwai wasu Fasinjoji da suka samu raunuka wadanda yanzu haka su ke karbar kulawar gaggawa a Asibiti. pindula.co.zw
Talla

Shalkwatar rundunar 'yansanda ta Zimbabwe ta ce fashewar wani abu da ake kyautata zaton tukunyar gas ce shi ne ya haddasa konewar motar da kusan dukkanin fasinjan da ke ciki.

A cewar Charity Charamba jami'ar yada labaran rundunar 'yan sandan ta Zimbabwe akwai tabbacin mutanen da suka mutu sun haura 42 da aka gano gawarsu la'akari da yadda wasu mutanen aka gaza gano gawarsu sakamakon kone kurmus.

Gidan talabijin mallakin kasar ya nuna hotunan motar a babbar hanyar da ke gab da kan iyakar kasar da Afrika ta kudu.

Sai dai jami'an tsaron sun ce akwai wasu Fasinjoji da suka samu raunuka wadanda yanzu haka su ke karbar kulawar gaggawa a Asibiti.   

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.