Emmanuel Macron zai gana da al Sisi a Masar
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai isa kasar Masar a wata ziyarar kwanaki uku, ziyarar da ake kalo a matsayin sake dawowa da kyaukiyawar hulda ta kasuwanci da diflomasiya tsakanin Faransa da Masar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Masar na daga cikin kasashen dake da kyaukiyawar hulda musaman bangaren tsaro da Faransa.
A gobe litinin ne Shugaba Macron zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah Al Sissi, a dai-dai lokacin da wasu kungiyoyin kare hakokin bil adam ke fatan Shugaba Macron zai ambato batutuwan da suka shafi kare hakokin bil adam a da shugaban Masar.
Faransa da jimawa ,na daga cikin kasashen dake sayarwa Masar da makamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu