Isa ga babban shafi
Sudan

An rufe makarantun Sudan saboda kashe dalibai

Hukumomin Sudan sun sanar da rufe makarantun kasar baki daya bayan da dalibai suka kaddamar da zanga-zangar adawa da kisan gillar da aka yi wa wasu masu zanga-zanga guda 6, cikin su harda 'yan makaranta guda 5.

Wasu daga cikin daliban Sudan rike da tutocin kasar a zanga-zangar da suka shiga bayan kashe 'yan uwansu dalibai.
Wasu daga cikin daliban Sudan rike da tutocin kasar a zanga-zangar da suka shiga bayan kashe 'yan uwansu dalibai. Ebrahim HAMID / AFP
Talla

Daruruwan daliban da suka shiga zanga-zangar gama-garin dauke da tutocin kasar, sun bayyana cewar kashe dalibi tamkar kashe kasa ne, inda suka yi jerin gwano a Khartoum da Omdurman da kuma sauran biranen kasar.

Rahotanni sun ce, dalibai 5 aka kashe yayinda sama da 60 suka samu raunuka lokacin da wasu maharba suka bude musu wuta a Al-Obeid, kisan da aka danganta shi da jami’an tsaron da ke kai daukin gaggawa.

Wannan kisan ya sa shugabannin masu zanga-zangar soke shirin ganawarsu da wakilan gwamnatin soji a kokarin da suke na kammala kafa gwamnatin rikon kwaryar da za ta kama aiki.

Hukumar Kula da Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bukaci gudanar da bincike kan kisan daliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.