Isa ga babban shafi

Tsadar rayuwa a Zimbabwe ta tilastawa ma'aikata zaman gida

Gamayyar Kungiyoyin ma’aikatan gwamnati a Zimbabwe ta ce ‘ya’yanta ba za su iya ci gaba, da zuwa ma’aikatunsu ba, saboda hauhawar farashin kayayayyakin bukata da ya tsananta a baya bayan nan.

Ma'aikatan lafiya a Zimbabwe
Ma'aikatan lafiya a Zimbabwe REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Kungiyar Kwadagon ta ce yanzu haka ma’aikata kimanin dubu 230 ne ba sa iya zuwa wuraren ayyukansu, saboda tashin gauron zabin da farashin kayan masarufi da sauran abubuwan bukata yayi.

Wannan al’amari dai, ya sake dora nauyi kan gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa dake kokarin warware matsalar tattalin arzikin da Zimbabwe ke fuskanta, musamman karancin kudadeb ketare, man fetur da kuma karancin biredi.

Sai dai, kungiyoyin sun ce za su jinkirta shiga yajin aikin da suka yi niyya, domin baiwa gwamnati lokacin fito da tsare-tsaren warware matsalar.

Rahotanni daga kasar ta Zimbabwe sun ce ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro ne ke ci gaba da aikinsu kamar yadda suka saba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.