Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Buhari ya fadi dalilansa na kin tsoma baki a rikicin Ganduje da Sarki

A ganawar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tawagar gwamnatin Kano da ta kunshi wasu sabbin ‘yan majalisu karkashin jagorancin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, shugaban kasar ya bayyana wasu daga cikin dalilin da ya hana shi tsoma baki a rikicin Gwamnan da Mai martaba sarki Muhamamdu Sanusi na II.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. ng.gov.jpg
Talla

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa karkashin kundin tsarin mulkin kasa, ba shi da hurumin tsoma baki a rikicin la’akari da yadda batun ke gaban Majalisar Jihar, matakin da ke nuna cewa Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje tare da Majalisar ne kadai ke da ta cewa.

Cikin bayanan wanda mai Magana da yawun shugaban Najeriya Garba Shehu ya rabawa manema labarai bayan ganawar a yau Juma’a, Muhammadu Buhari ya yi fatan kawo karshen matsalar a Kano, yayinda ya nanata matsayinsa na tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al’umma.

Takardar bayan taron nay au, ta kuma ruwaito shugaba Muhammadu Buhari na bayyana cewa baya fatan yiwa kundin tsarin mulkin kasar karantsaye wajen wuce makadi da rawa.

Rikici tsakanin gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje da mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi na II ya fito fili ne bayan da gwamnan ya dau matakin nadin sabbin sarakunan masu daraja ta 1 har guda 4 a jihar matakin da ke matsayin kishiya ga Sarki Sanusi duk kuwa da hanin hakan daga Kotu.

Sai dai a jawabin gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje bayan ganawarsa da Muhammadu Buhari a yau Juma’a ya ce matakin nadin sabbin sarakunan baya nufin raba kai ko kuma haddasa rudu tsakanin al’ummar kanawa.

Akwai dai zarge-zarge da ke nuna cewa Gwamnan na Kano na shirin tube rawanin Sarki Muhammadu Sanusi na II wanda ya maye gurbin Mai martaba Sarki Alhaji Ado Bayero da ya koma ga mahaliccinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.