Isa ga babban shafi
Guinea

Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar Equatorial Guinea ya haura 98

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Guinea ta tabbatar da mutuwar mutane 98 yayinda wasu 615 suka jikkata sakamakon tashin bama-bamai a sansanin soja na Nkoa Ntoma dake Bata, gari mafi girma a kasar.

Masu aikin agaji dauke da gawan wadanda suka mutu sakamkon fashewar da ta auku a barikin sojojin Equatorial Guinea
Masu aikin agaji dauke da gawan wadanda suka mutu sakamkon fashewar da ta auku a barikin sojojin Equatorial Guinea via REUTERS - REUTERS TV
Talla

Wadannan bama-bamai dai sun rusa gidaje da dama dake dabda sansanin sojan, dake nuna tamkar an yi kazamin yaki ne a yankin, yayinda maaikatan agaji ke ta kai dauki.

Ganau sun ce  har akwai wasu kananan yara 3 masu shekaru tsakanin 3-4 da aka zaro su karkashin fine-gine da sauran numfashi kafin agarzaya da su asibiti.

Sau 4 ne dai aakaji rugugin bama-baman tun da rana jiya lahadi, a daidai inda aka girke Dakarun musamman na kasar da Jandarmomi da kuma iyalansu, bayaga wasu rukunin gidajen jamaa.

Shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema wanda yake mulkin kasar na tsawon shekaru 42 ya danganta lamarin da tsautsayi da rashin kulawa na masu lura da rumbun ajiyan bama-baman.

Garin Bata masauki ne  ga mutane akalla dubu dari 8, daga cikin mutan kasar miliyan daya da dubu dari 4, kuma yawancinsu matalauta ne, duk da cewa akwai albarkatun mai da kuma iskar Gas a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.