Isa ga babban shafi
Chadi-'Yan tawaye

Sojojin Chadi sun nemi taimakon Nijar bayan kisan Deby

Gwamnatin mulkin sojin kasar Chadi ta bukaci mahukuntan Jamhuriyar Nijar da su taimaka mata domin cafke jagoran ‘yan tawayen kasar wanda yanzu haka ke fakewa a wani wuri da ke tsakanin garuruwan N’gourti da Nguinguimi a cikin kasar ta Nijar.

Dakarun Chadi sun daura damarar yaki da 'yan tawayen FACT da suka kashe shugaba Idriss Deby Itno
Dakarun Chadi sun daura damarar yaki da 'yan tawayen FACT da suka kashe shugaba Idriss Deby Itno AFP - RENAUD MASBEYE BOYBEYE
Talla

Kodayake jagoran ‘yan tawayen na FACT, Mahamat Mahdi Ali, ya musanta wannan ikirari da ke cewa ya tsere zuwa Jamhuriyar Nijar, inda ya ce yanzu haka yana nan cikin kasar ta Chadi a wani wuri da ke lardin Kanem.

'Yan tawayen sun bukaci zaman sulhu da sojojin, amma sanarwar da sojojin Chadin suka fitar ta bakin Janar Azem Bermandoa Agouna, ta yi watsi da tayin shiga tattaunawar saboda a cewarsu jagoran 'yan tawayen ya aikata laifufukan yaki ciki har da kashe Marshal Idris Deby Itno.

Agouna ya ce, " Chadi na kira domin samun hadin-kai da kuma goyon bayan kasar Nijar saboda cafkewa tare da mika wadannan mutane da suka aikata laifufukan yaki, wadanda suka kashe dakarun kasar Chadi da dama ciki har da Marshal na kasar Chadi, muna son kama su ne don  gurfanar da su gaban shari’a, a karkashin yarjeniyoyi da suka hada kasashen biyu."

"Lura da irin munanan laifufukan da suka aikata, da kuma kasancewarsu babbar barazana ga zaman lafiyar wannan yankin baki daya, Chadi, sam ba ta da niyyar shiga tattaunawa balantana sulhuntawa da wadannan miyagun mutane." inji Janar Agouna.

Chadi dai ta yi  kira ga illahirin kasashe mambobi a kungiyar G5-Sahel da su hada kai domin murkushe mutanen da suka kashe marigayi Idris Deby, sannan kuma suke ci gaba da kasancewar babbar barazana ga zaman lafiyar yankin Sahel baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.