An kori alkalin kotun kolin Equatorial Guinea saboda rashawa
Shugaban Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya ce ya sallami alkalin kotun kolin kasar biyo bayan amsa laifin karbar na goro a badakalar sauya lokacin lalacewar kayayyakin abinci da magunguna da ya yi.
Wallafawa ranar:
Shugaba Mbasogo, wanda ya shafe kusan shekaru 43 yana mulkin kasar ya sallami alklin kotun kolin, David Nguema Obiang Eyang ne sakamakon kama shi da laifin saba ka’idojin aikinsa.
Mataimakin shugaban kasar, Teodoro Nguema Obiang Mangue, wanda da ne ga shugaba Mbasogo ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Eyang ya amsa laifin karbar Cfa miliyan 100 a matsayin toshiyar baki daga wani babban kamfani a kasar.
Babu alamun da ke nuna cewa alkalin zai gurfana a gaban kuliya sakamakon wannan laifi da ya amsa.
An ci tarar kamfanin da ya bada wannan toshiya Cfa miliyan 411, kana aka lalata kayayyakin da aka sauya lokacin lalacewarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu