Isa ga babban shafi

Al'ummar Kenya na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

A yayinda al’ummar Kenya ke kada kuri’a a zaben shugaban kasa yau talata, hukumar zaben kasar ta soke wasu mazabu guda hudu tare da cafke jami’anta shida saboda zargin su da yunkurin magudi.

Dan takarar shugaban kasa a Kenya William Ruto.
Dan takarar shugaban kasa a Kenya William Ruto. REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Miliyoyin al’ummar Kenya ne dai ke kada kuri’a a zaben na shugaban kasa, inda manyan ‘yan takara biyu, wato mataimakin shugaban kasa William Rutto da jagoran ‘yan adawa, Raila Odinga ke fafatawa da juna.

Kazalika masu kada kuri’ar za su zabi gwamnoni da sanatoci da ‘yan majalisa har ma da shugabannin kananan hukumomi.

Hukumar zaben ta IEBC ta ce ta kama jami’an na ta ne saboda zargin cewa, sun gana da wasu ‘yan takara da zummar taimaka musu wajen murdiyar zabe.

Hukumar ta ce, ba za ta yi shayin daukar tsauttsauran mataki kan duk wani jami’inta da ya karya dokokinta ba, yayin da ta yi watsi da fargaba daa jama’ar kasar ke da ita kan magudi, tare kuma ta karfafa al’umma guiwar fita rumfunan zaben.

Har ila yau, hukumar ta baayyana cewa, ta dage zaben gwamna a lardunan Mombasa da Kakamega da kuma zaben ‘yan majalisa a Kachiliba da Pokot South har sai baba-ta-gaani saboda kura-kuran da ta ace, an samu kan takardun dangwalaa kuri’u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.