Isa ga babban shafi

Ruto na kan gaba a Kenya yayin da ake ci gaba da fitar da sakamakon zabe

Mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto na gaban babban abokin hamayyarsa Raila Odinga a zaben shugabancin kasar, lamarin da ya kara jaddada cewa har yanzu ba a kammala kirga kuri’un zaben ba, yayin da kasar ke dakon sakamako na karshe.

Mataimakin shugaban kasar Kenya na yanzu kenan, William Ruto
Mataimakin shugaban kasar Kenya na yanzu kenan, William Ruto REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Ruto ya samu kashi 51.25 cikin 100 na kuri’un da aka kada, inda Odinga ya samu kashi 48.09 bisa 100, a cewar alkaluman Hukumar Zabe mai zaman kanta ta IEBC, wadda ta fitar da sakamakon kusan kashi 50 na mazabu.

Zaben na ranar Talata ya gudana cikin kwanciyar hankali amma sakamakon zabukan da suka gabata da suka haifar da tashin hankali da sakamakon zargin yunkurin aikata magudi, abin da ya sanya hukumar ta IEBC fara fuskantar matsananciyar matsin lamba.

An girke ‘yan sandan kwantar da tarzoma cikin dare a hukumar da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya bayan da wakilan jam’iyyun siyasa suka fara kokarin haifar da tarzoma.

Shugaban hukumar, Wafula Chebukati a ranar Juma’a ya zargi wakilan jam’iyyu da jinkirta kidayar kuri’u ta hanyar cudanya da ma’aikatan zabe tare da jefa musu tambayoyin da ba su dace ba.

jinkirin dai ya jefa al’ummar Kenya cikin zulumi, inda da yawa ke fatan cewa duk wata takaddama kan sakamakon za a magance ta cikin lumana kuma ta hanyar doka.

A babban zaben dai ana fafatawa ne tsakanin Odinga, wanda tsohon madugun 'yan adawa ne kuma, a yanzu da ke samun goyon bayan jam'iyya mai mulki, da kuma Ruto, wanda ake kyautata zaton zai gaji shugaba Uhuru Kenyatta duk da cewa shugaban na Kenya ya hada kai da tsohon abokin hamayyarsa Odinga a wani gagarumin sauyi na kawancen siyasa.

Kasashen duniya da ke kallon Kenya a matsayin wani ginshikin zaman lafiya a yankin da ke fama da rikici, na sa ido sosai a zaben, inda sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana zaben kasar a matsayin abin koyi ga nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.