Malawi na fama da karancin alluran rigakafin kwalara bayan tsanantar cutar
Dai dai lokacin da Malawi ke fama da mafi munin annobar kwalara wadda ke ci gaba da kisa a sassan kasar, ma’aikatar lafiya ta sanar da karancin allurar rigakafin wannan cuta da ke sanya amai da gudawa.
Wallafawa ranar:
Kakakin ma’aikatar lafiyar kasar Adrian Chikumbe ya bayyana cewa kasar ba ta da wadatttun alluran rigakafin cutar ta kwalara a kasa da za ta yi amfani da su wajen dakile yaduwar cutar.
A watan Nuwamba ne Malawi ta karbi allurai miliyan 2 da dubu 900 daga kamfanin harhada magunguna na Gavi sai dai tsanantar cutar wadda ta fara bulla tun a watan Maris din bara cikin sassan kasar 29 ya haddasa karancin alluran.
Bisa alkaluman ma’aikatar lafiya a jiya juma’a dai kasar na da mutane 631 da suka mutu sanadiyyar cutar ta kwalara daga bullarta zuwa yanzu ciki har da wasu 17 da ta kashe a jiyan, yayinda a jummalla kasar ke da mutum dubu 28 da 132 da 916 wadanda ke jinyar cutar yanzu haka.
Ko a watan jiya sai da hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi kan yadda cutar ke tsananta a kasar, wadda ta ce wajibi ne a dauki matakan gaggawa don dakile yaduwarta zuwa sauran sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu