Isa ga babban shafi

Kwalara ta kashe sama da mutane dubu a Malawi

Alkaluman mutanen da cutar kwalara ta kashe a Malawi sun haura dubu guda, a daidai lokacin da adadin masu dauke da cutar ya karu zuwa dubu 30 da 600 daga lokacin barkewar cutar zuwa yanzu.

Kwalara na ci gaba da kisa a Malawi.
Kwalara na ci gaba da kisa a Malawi. AFP/File
Talla

Ma’aikatar Lafiyar Malawi ta ce, har zuwa yanzu babu alluran rigakafin cutar dalilin da ya sanya karuwar masu harbuwa da cutar a sassan kasar.

A watan Oktoban bara ne kasar ta kudancin Afrika ta samu bullar cutar ta kwalara mafi muni, lamarin da ya sanya Hukumar Lafiya ta Duniya aike mata da alluran rigakafi miliyan 3 a watan Nuwamba a wani yunkuri na dakile cutar.

Kakakin Ma’aikatar Lafiya a Malawi, Adrian Chikumbe ya ce, sun karar da dukkanin alluran rigakafin da aka bai wa kasar, a daidai lokacin da ake da tarin yaran da har zuwa yanzu ba a yi musu rigakafi ba.      

A cewar Chikumbe yanzu haka kasar na laluben inda za ta samu rigakafin cutar don tsiratar da dimbin al’ummarta da ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Bayan karuwar adadin mutanen da cutar ta kashe zuwa dubu 1 da guda 2 alkaluma sun nuna cewa a wannan karon cutar ta kwalara ta fi tsananta fiye da irin wadda aka gani a shekarar 2001, inda cutar ta kashe mutane 968.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.